fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Gidan Da Mafusata Suka KaiWa Hari A Bauchi Ba Na Shugaban INEC Ba Ne”

“Gidan Da Mafusata Suka KaiWa Hari A Bauchi Ba Na Shugaban INEC Ba Ne”

 

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa wani gida da hasalallun matasa su ka kai wa hari a Bauchi, ba na Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ba ne.

 

Hukumar ta ce ba Yakubu ne ke da gidan ba, a cikin wata sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na shugaban, Rotimi Oyekanmi ya fitar a ranar Asabar.

 

Jami’in yaɗa labaran ya ce Yakubu ba shi da gida a Bauchi, don haka masu cewa gidan ne, ji-ta-ji-ta ce kawai su ke yaɗawa don su ɓata masa suna.

 

“Gidan da aka nuno a soshiyal midiya, a cikin wani bidiyo da wasu matasa su ka kai wa hari, ba gidan Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ba ne.

 

“Shugaban Hukumar Zaɓe ba shi ke da wannan gida da aka nuno ba. Saboda haka bai mallaki wannan gida a Bauchi ko ma a wane gari ba a duniya.

 

“Danganta gidan da Shugaban INEC ci gaban wata maƙarƙashiya ce da yarfen da ake yi masa, domin su ɓata masa suna kawai. Wannan kuma duk aikin masharranta ne.

 

“Hukumar Zaɓe da shugaban ta na kira ga jama’a su yi watsi da masu yarfen cewa gidan shugaban hukumar ne aka kai wa hari, a Bauchi.”

 

….’Yan sanda sun ƙaryata labarin kai wa gidan Shugaban INEC hari

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa hasalallun matasa sun kai wa gidan Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu hari a Bauchi.

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

 

Tun daga ranar Juma’a ce aka riƙa yaɗa wani faifan bidiyo a soshiyal midiya, inda aka nuno cincirindon matasa a ƙofar wani gida su na jifa.

 

Gidan an riƙa danganta shi da cewa gidan Yakubu ne, Shugaban INEC da ke Bauchi.

 

Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil, ya shaida wa manema labarai cewa gidan ba na shugaban hukumar zaɓe ba ne.

 

Cikin sanarwar da Wakil ya raba wa manema labarai a ranar Asabar, ya bayyana cewa: “Mu na so mu fayyace wa jama’a wannan abu da ya faru ba ma a Jihar Bauchi ba ne kwata-kwata.

 

“Saboda haka danganta gidan da cewa na Shugaban INEC ko da ke Bauchi, ƙarya ce, jama’a su guje ta.

 

“Bisa la’akari da irin illar yaɗa irin waɗannan labarai na bogi, musamman a wannan lokaci na bayan kammala zaɓe, zai iya yin tasiri ko barazana ga zaman lafiya.

 

“Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ya bada umarnin a gaggauta binciken tushen bidiyon da aka riƙa yaɗawa har ana danganta ta shi da gidan Yakubu na Bauchi.”

 

Kwamishinan ‘yan sandan Aminu Alhassan ya ce wanda duk aka kama da laifi zai fuskanci hukunci a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *