fbpx
Friday, February 26
Shadow

Gidan yarin jihar Kaduna sun ki karbar me laifin da aka yakewa hukuncin shekaru 7

Gidan yarin jihar Kaduna sun ki karbar mutumin da aka yankewa hukuncin shekaru 7 a gidan yari daga Hannun hukumar hana rashawa ta EFCC.

Shugaban gidan yarin, Sanusi Dan Musa ya bayyana cewa daga sama ne aka hanasu karbar masu ziyara ko kuma sabbin masu laifi a cikin gidan yarin.

 

Ya kara da cewa an dauki matakinne dan kare mazauna gidan canja halin daga kamuwa da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Sadiq Mustapha wanda dan canji ne an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 7 ba tare da zabin biyan tara ba.

 

Da yake nuna rashin jin dadinsa kan lamarin, shugaban EFCC reshen jihar Kaduna, Yakubu Mailafia ya bayyana cewa wannan abu bai kamata ba. Yace suna da ka’idar ajiye me laifi kuma gidan yari shine waje na karshe da ya kamata a kai mai laifi.

 

Yace ya kamata ace a kowane gidan yarin Najeriya akwai gurin killace mutane masu cutar Coronavirus/COVID-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *