Jam’iyyar APC tayi tsokaci kan membobinda da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar abokan adawarsu ta PDP.
A wata wasika data fito daga hannun sakataren APC na jihar, Comrade Yusuf Idris Gusau yace sauya shekar tasu bata ragewa jam’iyyar komai ba.
Kuma yace girman kaine yasa suka ki sanar da jam’iyyar cewa zasu sauya sheka.
A karshe yace duk da haka dai APC dake mulkin jihar itace kan gaba kuma tana cigaba da tarbin sabbin membobin dake dawowa jam’iyyar a jihar.