Wani hoton bidiyo da ya watsu a kafafan sadarwa ya nuna wani masallaci mai dadaddan tarihi, da aka ginashi da Katakwaye tun a karni na 17 a zamanin sarki
Ottoman Sultan, na ci da wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa, an hangi hayaki a lokacin da ya turnike sararin sama a daura da yankin da Masallacin yake, kamar yadda wasu Majiyoyi suka tabbatar.
Hakanan Majiyoyin sun tabbatar da cewa, jami’an kashe gobara sun isa a kan lokaci wanda su ka shafe,wasu ‘yan sa’o’i suna kokarin shawo kan al”amarin.
Sai dai har zuwa wanan lokaci hukumomi ba su bayyana Musabbabin tashin gobarar ba.