fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gobara Ta Tashi a Fadar Ooni Of Ife a Jihar Osun

Rahotannin sun nuna cewa gobara ta tashi a Fadar Ooni na Ife a Jihar Osun, Oba Adeyeye Ogunwusi.
Wutar da ba a kai ga kashe ta ba ta tashi ne a daya daga cikin gine-ginen da ke fadar basaraken.
Wata majiya ta ruwaito Jami’in Gudanarwa da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun, Fatai Aremu, ya tabbatar da tashin gobarar.
Ya ce jami’an hukumar sun isa fadar Oba Adeyeye Ogunwusi domin kashe wutar da ta tashi.
Wasu rahotanni na cewa “wutar ba mai tsanani ba ce, sai dai mutane sun razana saboda kasancewar kofar shiga fadar a kulle”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published.