Wani kamfanin kera kayayyaki polythene ya kama da wuta wanda ke daura da Ahmmadiya Bus Stop, yankin Abule-Egba na jihar Legas.
Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ba a sami wani wanda yarasa ransa ba.
An samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar yayin da kamafanin ke gudanar da aikin samar da kayayyaki a masana’antar da ke kan titin Wifunke, dake bayan gidan mai Abule-Egba.
A cewar wasu ma’aikatan da ke cikin masana’antar, sun bayyana cewa wutar ta tashi ne daga wani sashin gudanarwa dake cikin kamfanin saboda matsanancin zafi.
Daga bisani ma’aikatan kashe gobara sunyi nasarar kashe wutar hadi da taimakon jami’an ‘yan sanda wajan bada kariya a lokacin faruwar Lamarin.