Gobara ta tashi a yau Juma’a a wani rukunin shaguna a Dahran da ke gabashin Saudiyya.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa babu wanda ya rasu ko kuma ya samu rauni.
A wani saƙo da hukumar da ke kare farar hula ta ƙasar ta wallafa a shafin Twitter, ma’aikatar ta ce masu aikin kashe gobara tare da taimakon jirgi mai saukar ungulu sun yi ƙoƙari sun kashe wutar.
Babu tabbaci kan yadda gobarar ta tashi amma ana gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar.