Gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yayi gobara. Gidan dake birnin Abeokuta na jihar Ogun ya kama da wutane da misalin karfe 10 na daren Laraba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Rahotanni sun tabbatar da cewa wutar lantarki ce ta yi sanadin gobarar.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin. Jama’ar gari sun taimakawa ma’aikatan hukumar aka kashe gobarar.
Obasanjo ya zauna a gidan lokacin yana shugaban kasa kamin daga baya ya koma gidan dake harabar dakin karatu na shugaban kasa dake jihar.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole