fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Mata A Garin Yawuri

Daga Sani Twoeffect Yawuri

A daren jiya Laraba 19/01/2022 an samu tashin gobara a wani gida dake tashar Kattai a cikin garin Yawuri dake jihar Kebbi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar miji da mata, kuma Allah ya tseratar da Ɗan ƙaramin yaron su.

Gobarar dai ta tashi a dakin marigayi Malam Babangida da matar sa a tsakiyar dare, misalin karfe 02:00, inda shida mai ɗakin sa suka yi kokarin fita daga cikin dakin, sai dai wutar ta rinjaye su, amma cikin ikon Allah da yardar sa sun samu nasarar kuɓutar da ɗan karamin yaron su inda suka turo shi ta tagar dakin da yakama da wutar

Karanta wannan  Shugabar Kungiyar Taimakon Yara Da Mata Mabukata Ta Kasa Ta Rasu Sakamakon Mummunan Hadari

Tuni dai aka yi jana’izar su kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Muna addu’ar Allah Ya jikan su da rahamar sa, kuma ya albarkaci abunda suka bari, mu kuma ya kyautata namu karshe bayan nasu. Amin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.