fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Gobara tayi sanadin mutuwar Jariria sabbin haihuwa a kasar India

Wani Al’amari mai cike da ban tausayi da kuma Al’hini da ya faru a wani Asbitin gwamnati dake a yammacin Indiya inda gobara tai sanadin mutuwar wasu jariria har guda 10 al’amarin da ya sanya rudani a cikin zukatan Mazauna yankin.

Lamarin Dai Ya faru a ranar Asabar a wani Asbiti dake Bhandara wanda ke a  jihar Maharashtra dake can kasar ta Indiya.

A wani rahoto da aka bayyana da  cewa, a lokacin da gobarar ta tashi akwai a kalla jarirai 17 a sashin kula da masu sabbin haihuwa, yayin da 10 daga ciki aka rawaito sun mutu a sakamakon hayaki da ya turnike sashin da jaririn ke kwance, inda wasu kuma suka rasa ransu a sanadin raunin kona da suka samu yayin da ragowar Jariran 7 Ma’aikatan Asbitin suka kai ga nasarar cetowa.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Shugaban karamar hukumar mahaifar Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar NNPP

Sai dai biyo bayan Al’marin Tuni Dai Gwamnati ta bada Umarnin bincikar Musabbabin da ya haddasa tashin gobarar a Asbitin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.