Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yayi Magana kan tsayawarsa takara a shekarar 2023.
Ana ta dai jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar, Goodluck zai tsaya takara a shekarar ta 2023 imda har ake rade-radin cewa zai koma jam’iyyar APC.
Saidai Jonathan a martaninsa kan wannan lamari yace shaci fadin wasu mutanene kawai. Ya kuma jinjinawa shugaba Buhari akan kokarin da yake kan tsaro.