fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gowon ya karyata ikirarin Majalisar Dokokin Burtaniya cewa ya ‘saci rabin kudin Babban Bankin Najeriya zuwa Ingila

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Yakubu Gowon, ya musanta zargin da ake yi masa cewa ya kai “rabin kudaden Babban Bankin Najeriya kasar ingila”.
Wani dan majalisar dokokin Burtaniya, Tom Tugendhat, ne ya yi wannan ikirarin yayin muhawara kan harbe-harbe da akayi Lekki ga masu zanga-zanga.
Tugendhat ya ce “mun san cewa a yau, ko da a yanzu, a cikin wannan babban birni namu, akwai, abin bakin ciki, wasu mutane da suka karɓa daga mutanen Najeriya suka ɓoye ribar da suka samu a nan.” Ya ce Gowon yana daya daga cikinsu. A cewarsa, Gowon ya dauki rabin CBN zuwa Ingila.
Sai dai kuma, a wata hira da BBC, Gowon ya bayyana zargin a matsayin “karya”.
Ya ce: “Abin da dan majalisar ya fada karya ne. Ban san daga ina ya samo wannan shara ba. Na yi wa Najeriya aiki tukuru kuma bayanan na nan kowa ya gani.
“Ba na son yin magana a kan wannan batun saboda mutanen da suka san ni sun san cewa abin da dan majalisar ya fada ba gaskiya ba ne.”
Gowon ya kasance Shugaban Kasar daga 1966 zuwa 1975.

“What we are seeing in Nigeria today is part of that story. It is a tragedy we are all witnessing because we see things falling apart.

“The problem this time is not foreign pressure known as colonialism. The pressure instead is corruption and violence and attempts at control (of power).

“We need to call out the corruption, we need to use the powers that we have in this country to stop those who are profiting from the wealth of that great nation and hiding it here.

“Now some people will remember when general Gowon left Nigeria, he took half of the Central Bank, so it is said, and moved to London.

“We know today, even now in this great city of ours, there are sadly some people who have taken the wealth of Nigerian people and hidden their ill-gotten gains here.

“We know that our banks sadly have been used for that profit or that illegal transfer of asset and that means that the UK is in a unique position in being able to actually do something to really exert pressure on those who have robbed Nigerians.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan ta'adda sun kaiwa 'yan mahalissar jihar Baushi hari sun ji masu rauni tare da bata masu kadarori su yayin da suke gudanar da taro

Leave a Reply

Your email address will not be published.