fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Gumi Ya Jagoranci Shugabannin Addini Zuwa Gidan Obasanjo Kan Matsalar Tsaro

Shahararren malamin addinin Islama, Sheik Ahmad Gumi, yanzu haka yana cikin ganawa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta na jihar Ogun.
Gumi, ya isa gidan tsohon shugaban wanda ke da dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, da misalin karfe 11 na safe, kuma kai tsaye ya shiga taron.
Mai taimaka wa Obasanjo kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi, wanda ya tabbatar da haka ga Aminiya, ya ce wasu shugabannin addinai ma na halartar taron.
“Ee, gaskiya ne. Shi (Gumi) yanzu haka yana ganawa da Baba tare da sauran shugabannin addinai, ”in ji Akinyemi.
A kwanakin baya malamin ya hadu da kungiyoyin ‘yan fashi a jihohin Zamfara da Neja don sasanta wadanda aka sace.
Gumi ya roki gwamnati da ta yi wa ‘yan fashin afuwa, Wanda hakan ya jawo kace nace a duk fadin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  A rika sanar dani daga yau domin ba zan laminci kashe mutane a kudu maso gabashin Najeriy ba, cewar shugaba Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.