Wannan wani gajeren hoton bidiyone da kafar labarai ta bbc ta wallafa wanda ke nuna wani gurin shan shayi da kayan tande-tande na zamani a lasar Tanzaniya wanda duka ma’aikatan gurin kuramene,basa jin magana.
An bude wannan gurinne saboda a kawar da nuna banbanci da kyama a akewa kuramen wajan samun aikinyi.
Wani ma’aikacin gurin wanda shima kurmane ya bayyana cewa yaje gurare da dama neman aiki amma saboda shi kurmane ba’a bashi aikinba, yace abin ya dameshi amma yanzu hankalinshi ya kwanta gashi yana aiki yana jin kanshin kamar sauran mutane kuma ga abokan aikinshi masu yanayi irinshi.
A cikin gurin shan shayin anyi wani allo inda aka rubuta alamomin yanda ake magana da kurame dan mutane masu zuwa gurin su koya.
Wannan abu ba karamin birge mutane yayi ba.