Kungiyar Burnley ta nada tsohon tauraron dan wasan Manchster City Vincent Komapany a matsayin sabon kocinta.
Kungiyar batada kocin na dindindin tun bayan data kori Sean Dyche a watan Afrilu.
Kuma ta nada Mike Jackson amma duk haka ya kasa jagorantar kungiyar inda ta fada Relagation a wasanta na karshe a wannan kakar.
Sabon kocinta Kompany zai fara horas da ita ne bayan ya bar kungiyar dayake horaswa ta Anderlecht.