Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu kan kudurin dokar ba da ilimi kyauta kuma wajubi a jihar.
Ganduje ya sanya hannu kan kudirin dokar ne, a gidan gwamnatin jihar a ranar Laraba.
Ana sa ran dokar zatai aiki ne akan kowane yaro da ya isa zuwa makaranta, inda aka bukaci iyaye da wajubi su sanya yaran su a makaranta.
Hakanan dokar za ta hukunta dukkan wasu iyayan da su ka ki tura yaran su makaranta.