Daga Muhammad Dahiru Shugaba
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi tattaki zuwa unguwar Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza, domin sa ido kan yadda za a tsugunar da iyalai 2,500 da suka rasa matsugunansu zuwa gidajensu da gwamnatin jihar ta sake ginawa.
‘Yan Boko Haram sun lalata gidajen a lokacin da suke mamaya, lamarin da ya tilastawa mazauna garin zama ‘yan gudun hijira a garin Pulka da ke wani gari a Gwoza, tare da samun mafaka a makwabciyar kasar Kamaru. Kirawa ya zama ba kowa fiye da shekaru shida.
Gwamna Zulum ya kafa wani kwamiti mai aikin sake gina gidajen da aka lalata a garin Kirawa da kuma dawowa lafiya bisa radin kansa da mutunci.
Zulum, a lokacin da ya yi tattaki na sake tsugunar da jama’a, ba wai kawai ya tabbatar da komawar gidajen da aka gina ba, ya kuma sa ido a kan rabon N120m ga iyalai 2,500.
Mazajen gidaje an baiwa kowannensu Naira 100,000 yayin da matansu (wasu daga cikin gidajen da suka amfana) an baiwa kowannen su N20,000.
Bugu da kari, dukkan magidanta 2,500 kowannen su ya samu kayan abinci da suka hada da buhun shinkafa, buhun gasar masara da kuma nade kowacce na matan da suka dawo.
Da yamma ne Gwamnan ya dawo Maiduguri. Ya yi tattaki ne tare da shugaban kwamitin sake matsugunin Kirawa, Engr Saleh Vungas wanda ya fito daga Gwoza kuma shi ne tsohon kwamishinan gidaje da makamashi na Zulum.
Tawagar ta kuma hada da dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltar karamar hukumar Gwoza, Abacha Buba, tsohon kwamishinan noma, Engr. Bukar Talba da sakataren din-din-din na ma’aikatar yaki da fatara da sauran jami’an gwamnati.