fbpx
Tuesday, August 4
Shadow

Gwamantin Jihar Sokoto Ta Fitar Da Farashin Takin Zamani Na Wannan Shekaran

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ba da sanarwar sayar da takin zamani a tallafin kudi na Naira 4,000 a kowace jaka.
Tambuwal, yayin da yake ba da sanarwar sayarwa da rarrabawa a shagon sayar da kayan aikin gona, a Kasarawa, a karamar hukumar Wamakko, ya ce manufar ita ce bunkasa harkar noma, rage talauci da samar da ayyukan yi a jihar.
Gwamnan ya ba da sanarwar cewa jaka daya ta kilo 50 na nitro, phosphorus, potassium wanda aka samo daga Gwamnatin Tarayya akan farashin Naira 4,500 zai sayar a kan Naira 4,000, yayin da Urea wanda aka samo akan Naira 9,800 a kasuwa za’a siyar akan Naira 5,000 akan jaka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *