fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Gwamna Abudullahi Umar ganduje ya gana da shugabannin kiristoci dake jihar kano CAN

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nemi goyon bayan shugabanin kungiyar Christain Association of Nigeria (CAN) a cikin jihar domin shawo kan yaduwar cutar COVID-19.

Ganduje, wanda ya gana da shugabannin kungiyar a Gidan Gwamnati, Kano, ranar Talata, ya ce hadin gwiwar masu ruwa da tsaki ya zama dole domin dakile yaduwar cutar.

Gwamnan ya yi kira ga shugabanni da sauran mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan ga matakan kula da lafiya.

Gwamnan ya yabawa shugabancin kungiyar CAN sabuda rashin nuna banbanci a zamantakewa.

Shugaban CAN na jihar, Rev. Samuel Adeyemo, ya godewa gwamnan tare da yaba masa kan kokarin da yake wajan dakile yaduwar cutar a jihar Kano.

A karshe gwamanan kano yayi al’kawarin Samar da cibiyar gwaje-gwaje a yankin sabon gari dake jihar Kano

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *