fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Gwamna Almakura na jihar Nasarawa ya cikawa wata almajira burinta: Ya sai mata sabuwar mota da kyautar dubu dari biyu: Bayan daya ganta ana turata a baro

Gwamna Umar Tanko Almakura na jihar Nasarawa yayi wani abin yabo da aka rika jinjinamai akai, Gwamnan yana tafiya da tawagarshi a cikin garin Lafiya sai yaci karo da wani bawan Allah yana tura wannan matar da ake gani a cikin baro.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Matar me sun Fatima Musa ta fitone daga jihar Bauchi kuma bara takeyi a jihar ta Nasarawa, gwamnan ya fito daga mota ya baiwa matar sadaka kuma ya tambayeta idan tana da wani abu da take da bukata.
Kada bakin Fatima sai tace burinta shine ta samu mota, a daina turata a baro, da gwamnan yaji haka, sai yayi murmushi, ya bayar da Umarnin a kaita gidan gwamnati washe gari.
Da gari ya waye aka dauki Fatima aka kaita godan gwamnatin jihar Nasarawa, kamar yanda NTA ta ruwaito, anan gwamna Almakura ya bata kyautar sabuwar mota, Toyota Corolla da kuma kudi naira dubu dari biyu, tasha mai.
Gwamnanne da kanshi bayan, Fatima ta shiga mota, ya daura mata beldin kujerar motar, aka dauki baronta aka saka a bayan motar, suka dauki hanyar Bauchi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tinubu ya gana da sarakunan gargajiya a fadarsa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *