Gwamnonin yankin Yarbawa 2, wanda tsohon gwamnan jihar Ogun ne amma a yanzu sanatane, Ibikunle Amosun da Kayode Fayemi wanda gwamnan jihar Ekitine zasu fito takarar shugabancin Najeriya.
Tuni dai sun sanar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya kuma ya musu fatan Alheri.
Yanzu akwai mutane 4 kenan daga kasashen Yarbawa da suka fito neman shugabancin Najeriya.
Watau Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Bola Ahmad Tinubu, da wadanan guda biyun.