Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Muhammad Abubakar ya ba da kyautar motar bas mai daukar mutane 36 ga kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Stars FC.
Kyautar ta zo daidai da kudirin da gwamnan ke yi don taimaka wa ƙungiyar wajan kai bantanta a kakar wasan kwallan kafa na kasa.
Shugaban kungiyar Abubakar Sadik ya gode wa gwamnan bisa goyon baya da kwarin gwiwa da yake nuna wa kungiyar, sannan ya kara da cewa motar za ta kara musu kwarin gwiwa don cimma kaiwa wani matsayi mai kyau a kakar wasan.