fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamna Badaru ya bayyana mutane 25 ne suka mutu sanadin Ambaliyar ruwa a jihar Jigawa

Ruwan sama ya yi sanadiyyar rayuka 25 a Jigawa

 

Akalla mutane 25 suka mutu sannan sama da gidaje 51,000 suka lalace sakamakon mamakon ruwan sama a Jigawa.

Gwamna Muhammad Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Dutse.

Gwamnan, duk da haka, ya ce ba zai iya bayar da takamaiman Al’kaluman adadin wadanda suka mutu ba a sakamakon mamakon ruwan da ke cigaba a jihar.

 

Hakanan Gwamnan ya jajantawa wadanda abun ya shafa tare da daukan al’washin cewa gwamnati za tai iya nata kokarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.