Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amince da sauya sunan jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur (Sa’adu Zungur University).
Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba a Bauchi, Kwamishinan Ilimi na jihar, Dokta Aliyu Tilde, ya ce an amince da sauya sunan ne a yayin taron Majalisar Zartaswa ta jihar wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Bauchi.
A cewar Mista Tilde, daga yanzu za’a fara kiran makarantar kamar da “Sa’adu Zungur University,” SAZUG, Gadau.
Ya ce sauya sunan ya biyo bayan bukatar tunawa Mista Zungur wanda ya mutu a 1958.