‘Yan majalissar jihar Kaduna sun roki tsohon shugaban APC wanda ke neman takarar shugaban kasa, Tinubu cewa ya zabi gwamna El Rufa’i a matsayin mataimakinsa.
A ranar alhamis data gabata Tinubu ya ziyarci Kaduna domin ganawa da wakilau 66 na jihar cewa su zabe shi a zaben fidda gwani da za’ayi.
Inda dan majalissar dake wakiltar Sabon Gari Garba, Babawo ya bayyana cewa suna rokon wata alfarma a wurin Tinubu wacce basu sanar da El Rufa’i ba domin ba zai amince ba.
Cewa don Allah ya zabi gwamna El Rufa’i a matsayin mataimakin shi a zaben shekarar 2023 saboda su san cewa gwamna kasar waje zai tafi da zarar ya sauka a mulki, amma su suna so ya cigaba da yiwa Najeriya hidima.