fbpx
Friday, December 2
Shadow

Gwamna El Rufa’i na kara taimakawa harkar matsalar tsaro a jihar Kaduna, cewar Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa gwamnan jiharsa ta Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i na taimakawa harkar matsalar tsaro.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a ranar lahadi yayin dayake ganawa da manema labarai na Arise,

Inda yace masu wasikar da El Rufa’i ya turawa shugaba Buhari ta cewa ‘yan bindiga na gina sansani a jihar ta nuna cewa gwamna El Rufa’i ya gaza kare rayukan al’ummarsa

Kuma ya turawa shugaba Buhari wannan wasikar ne domin ya wanke kansa a cikin harkar matsalar tsaro alhalin yana taimaka masu domin basa sanar da shugaba gaskiyar abinda ke faruwa a jihohinsu.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *