Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ya bayyana cewa an zabi shugaban kungiyar kamfe ta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC,
Wato Bola Ahmad Ahmad da kuma mataimakinsa Kashim Shetiima a taro da suka gudanar a babban birnin tarayya Abuja ranar litinin.
Inda yace sun gana da dan takarar da kuma mataimakinsa tare da sauran gwamnoni da kuma masu hannu da tsaki a jam’iyyar.
Amma yace ba zasu bayyana wanda suka zaba fili ba har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi akan zabin nasu.