fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Gwamna El-Rufai yace makarantu ma su rika aiki ranaku 4 a sati banda Juma’a

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya umarci makarantu da su koma aikin kwanaki 4 kawai a sati kamar yanda sauran ma’aikatan jihar Keyi.

 

Yace hakan zai baiwa malamai damar yin noma.

 

Yace hakan kuma zai baiwa ma’aikata damar samun lokacin iyalansu sannan yanayin aikin zai inganta.

 

Wannan umarni na zuwane yayin da makarantu ke komawa ci gaba da karatu ranar 10 ga watan Janairu.

 

Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal ce ta bayyana haka ga manema labarai ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published.