fbpx
Monday, August 8
Shadow

Gwamna Fintiri ya hana masu babur mai kafa uku da babura yin acaba a Yola

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bayar da Dokar Zartarwa ta hana amfani da babura masu kafa uku da babura da daddare a kewayen babban birnin jihar Adamawa wato Yola.

Haramcin ya shafi masu amfani da shi a cikin kananan hukumomin uku wadanda suka hada da Girei, Yola ta Arewa da Yola ta Kudu daga karfe 10 na dare zuwa 5 na safe.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na Gwamnan Fintiri Mista Humeashi Wonosikou a jiya.

Gwamna ya bayyana hakan a matsayin hanyar magance matsalar tsaro a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.