Ganduje ya amince da naira biliyan N4.66 don ciyar da dalibai A yayin da makarantu za su bude
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da kashe naira biliyan N4.66 don shirin ciyar da daliban makarantun firamare da na sakandare a jihar a shirye shiryen sake bude makarantu.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’ad Kiru, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Kano yayin bikin bude wani taron kara wa juna sani game da matakan kariya daga cutar COVID-19 ga shugabannin makarantu wanda aka gudanar a Ma’aikatar Ilimi.
Kwamishinan ya yi kira ga shugabannin makarantun da su tabbatar an ciyar da daliban da ingantaccen abinci, yana mai gargadin cewa ba za a amince da karkatar da kayan abinci ko kudaden da gwamnati ta bayar don shirin ciyar da dalibai.
Malam Sa’ad Kiru ya kuma bayyana cewa, shirye-shirye sun yi Nisa domin biyan malamai alawus da sauran hakkokinsu.