fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamna Ganduje ya bayyana matsayar gwamnati akan bude makarantun jihar

Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya bayyana matsayar gwamnatin jihar kano kan makarantun jihar da ke cigaba da ka sancewa a rufe tun tsawan lokacin da aka sanya dokar zaman gida a jihar a sakamakon bullar cutar Korona.

Gwamna ganduje ya bayyana cewa dukkan makarantun jihar zasu cigaba da kasancewa a rufe har zuwa wani lokaci da gwamnati zata bayyana,

A ranar Al’hamis ne gwamnatin jihar ta janye dokar zaman gida data sanya wanda ya shafe tsawan lokaci.

Bayan soke dokar zaman gida da gwamnatin jihar tai, haka zalika gwamnatin jihar ta Umarci ma’aikatan gwamnati da su koma bakin aiki su a ranar litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.