Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a jiya, Talata, ya kaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari maganar hukuncin kisan da aka yankewa matashinnan da yayi kalaman batanci ga Annabi(SAW).
Matashin, Yahaya Aminu Sharifai yayi wakane wadda ta watsu sosai a shafukan sada zumunta kuma Fusatattun matasa suka rusa gidansu, an kamashi aka kaishi kotun shari’ar Musulunci inda aka yanke masa hukuncin kisa bayan samunsa da laifi.
Saidai hakan ya jawo cece-kuce musamman daga kungiyoyin dake ikirarin kare hakkin bil’adama. Gwamna Ganduje ya bayyanawa manema labarai bayan ganawa da shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya cewa, matashin ya daukaka shari’a.
Yace ya kuma yiwa shugaba Buhari godiya bisa taimakon da ya baiwa jihar Kano na yaki da cutar Coronavirus/COVID-19, sannan kuma yawa shugaban jawabi game da harkar tsaron jihar.