fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Gwamna Ganduje ya zaɓi mataimakinsa Nasiru Gawuna don ya gaje shi

Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya zaɓi mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a babban zaɓe na 2023.

Wasu majiyoyi a Fadar Gwamnatin Kano sun shaida wa BBC Hausa an cimma matsayar ce yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulkin Kano da aka gudanar a yau Asabar.

Sai dai wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta faɗa wa BBC Hausa cewa har yanzu ba a kai ga daddale wannan zaɓi ba a hukumance.

Kazalika, an ruwaito cewa taron ya amince Kwamashinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu Murtala Sule Garo ya zama mataimakin Gawuna a takarar tasu.

Karanta wannan  Shugaba Buhari na ziyara a jihar Kano

Ana kallon matakin a matsayin wani sauyi daga goyon bayan da Murtala Garo ke samu na wasu jiga-jigan gwamnatin, ciki har da matar gwamna Hajiya Hafsat Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin Ganduje.

Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar wa ɓangaren Ganduje shugabancin APC a Kano sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaɓukan shugabanci a watan Oktoba tsakaninsa da ɓangaren tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.