Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya amince ya zabi musulmi a matsayin abokin takararsa.
Yace sun shawarce shi ya zabe musulmi ne a taron da suka gudanar a gidan gwamnan jihar Kano, kuma ya amince,
Yayin da Gnndujen yayi kira ga malaman Kano cewa su taya shi addu’a yayi nasara a zaben da kuma dan takarar gwamnan Kano bakidaya, watau mataimakinsa Yusuf Gawuna.
Ganduje yace zabar Musulmi a matsayin abokin takara ba sabon abu bane a kasar Najeriya, saboda haka hakan za ayi.