fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Gwamna Ganduje yayi kira da gwamnatin tarayya ta hana fulani shigowa Najeriya daga kasashen waje

Gwamnan jihar Kano,Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa yana kira ga gwamnatin tarayya data hana shigowar fulani makiyaya dake shigowa Najeriya daga kasashen waje.

 

Ganduje yayi kira da a sake duba yarjejeniyar zirga-zirga dake tsakanin kasashen Africa ta yamma.

Yace irin wadannan fulani dake shigowa Najeriya da makamai ne ke kawo matsalar tsaro kuma musamman wannan yawon da suke zuwa guri-guri na taimakawa wajan tada zaune tsaye.

 

Gwamna Ganduje ya bada wannan shawarane a lokacin da yake kaddamar da gidajen Ruga a Dansoshiya dake Kiru.

 

Yace irin wannan yunkuri zai bayar da dama ga fulani su zauna a waje daya maimako  yawace’yawace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *