A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da daukar ma’aikata kai tsaye ga dalibai 196 da suka kammala karatu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Nguru.
Buni, a wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da hulda da manema labarai Alhaji Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu, ya ce samar da ayyukan yi ga jami’an lafiyar zai bunkasa fannin kiwon lafiya.
Ya kara da cewa ma’aikatan sun hada da kwararrun likitocin harhada magunguna 23, kwararrun dakin gwaje-gwaje na likitanci 60, kwararrun likitocin aikin tiyatar hakori 62 da kwararrun kula da bayanan lafiya 51.