fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamna Mai Mala Buni ya nemi agaji wurin gwamnatin tarayya bayan ruwan sama ya tafi da gidaje, dabbobi tare da gonakin al’ummar jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya nemi agaji a wurin gwamnatin tarayya da hadin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta NEMA.

Gwamnan ya nemi agajin ne sakamakon ruwan sama daya saka wasu daga cikin al’ummar jihar cikin wani mawuyacin hali bayan ya shafe masu dukiyoyinsu.

Mai magana da yauwm gwamnan Mamman Muhammad ne ya bayyana hakan, inda yace musamman a Gujba da kuma Gulani ne wannan iftila’in ya faru.

Kuma gwamnan jihar ya tausayawa al’ummar jihar da wannan abin ya faru dasu sannan yasha alwashin cewa gwamnati zata tallafa masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.