Gwamna Masari Ya Baiwa Rarara Da Baban Chinedu Kyautar Naira Miliyan 80 Bayan Ƙona Masu Gidaje A Kano
Daga Comr Nura Siniya
Gwamnatin jihar Katsina ta baiwa mawaƙan APC Adamu Abdullahi Rarara da Yusuf Baban Chinedu tallafin kyautar zunzurutun kuɗi naira miliyan 80, sakamakon ƙona masu gidaje da aka yi a zaɓen da ya gabata na 2023.
“A cikin wata wasiƙa da aka aikewa babban Akanta Janar na Ma’aikatar Kudi ta Katsina, ta bayyana cewa Naira miliyan 50 na Dauda Adamu Abdullahi ne yayin da Naira miliyan 30 za ta tafi ga Baban Chinedu, domin biyan diyya ga mawaƙan bisa ɓarnar da aka musu na ƙona masu gidaje a jihar Kano.
Idan ba a manta ba, wasu fusatattun matasa sun ƙona gidan Rarara da Baban Chinedu, jim kaɗan bayan sanar da nasarar Abba Gida-Gida a zaɓen gwamna da ya gabata na 22, ga watan Maris 2023 a jihar Kano.
A rahoton da muka samu ya bayyana cewa an baiwa akanta Janar na jihar Katsina umarnin cewa a gaggawa biyan mawaƙan Rarara miliyan 50 sai Baban Chinedu Miliyan 30 domin rage asara.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda gababnin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29th ga watan Mayun 2023.