Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya biywa malamai 97 kujerar hajji domin su yiwa jihar addu’a akan kawo karshen ‘yan bindiga.
Mataimakin gwamnan, Hassan Nasiha ya kwadaitar a malaman cewa suyiwa jihar dama kasa Najeriya addu’ar zaman lafiya mai dorewa idan sun isa Makkah da Madina.
Kuma kafin tafiyarsu malan Dr. Atiku Balarabe yayi wayar masu dai akan yadda zasu gudanar da addu’o’in nasu a kasa mai tsarki.