Gwamnan jihar Zamfara, Hon. Bello Mohammed Matawalle ya ce bai yi wani shiri da kowa ba don sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar ta hannun Darakta-Janar, harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a na gidan Gwamnatin, Hon. Yusuf Idris Gusau.
A cewar sanarwar, Matawalle ya bayyana mutanen da ke yada labarin da ba shi da tushe ballantana makama a matsayin gigantattun yan siyasa, yana mai cewa ya kamata a jefa irin wadannan jita-jitar a cikin kwandon shara.
Gwamnan ya ce; ban tattauna wata magana ta sauya sheka zuwa APC da kowane dan siyasa ba a cikin jihar ko kuma wani wuri, babban burina yanzu shi ne maido da zaman lafiya a jihar wanda ya ɓace a lokacin mulkin APC.
Gwamna Matawalle ya ce mashahuran ‘yan siyasar da ba su da farin jini kamar Sagir Hamidu da ke yada wannan labari su jira har sai ya sauya sheka kafin su ce komai game da gwamnatinsa.
Duk da haka, Gwamnan yace akwai wasu jiga-jigan APC da ke nemansa ya sauya sheka zuwa APC amma har yanzu bai yanke shawarar hakan ba.
Ya ce mambobin APC da suka sauya sheka zuwa PDP sun lura cewa shugabannin APC a jihar ne ke haifar da rikice-rikicen da ke faruwa a cikin jam’iyyar, kuma damar da APC ke da ita na dawo da jihar a 2023 ba tabbas, shi yasa suka sauya sheka zuwa PDP.