fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Gwamna Matawalle ya tsige sarkin jihar Zamfara akan mulki bayan ya baiwa kasurgumin dan bindiga sarauta

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da sarkin Sabon Garin Yandoto, Alhaji Aliyu Garba Marafa dake karamar hukumar Tsafe.

Gwamnan ya dakatar da shine biyo bayan baiwa tubabben dan bindiga, Adamu Aleiro sarautar sarkin Fulanin na Yandoto.

Kuma ya bayar da umurni cewa a bincike sarkin kan wannan nadin daya yi duk da cewa manyan jami’ai sun hallaci taron.

Skataren gwamnatin jihar, Kabiru Sardauna ne ya bayyana hakan ranar lahadi, inda yace yanzu an baiwa Alh. Mahe Garba Marafa sarautar na rikon kwarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.