fbpx
Friday, October 23
Shadow

Gwamna Sule ya samu tikitin APC a Nasarawa kai tsaye don takarar zaben 2023

Jam’iyyar APC a Nasarawa ta tsayar da Gwamna Abdullahi Sule a matsayin dan takararta tilo a shekarar 2023.

Jam’iyyar ta bayyana cewa babu wani dan jam’iyyar a jihar da zai yi takara da Gwamna a 2023.
Sule ya sami wannan amincewar ne a karshen mako lokacin da masu ruwa da tsaki daga shiyyar sanata ta yamma karkashin jagorancin Gwamnan farar hula na farko kuma sanata mai wakiltar shiyyar, Abdullahi Adamu, ya ba da tabbacin babu wani dan jam’iyyar daga yankin da za su fafata da shi da zai zo 2023.
Masu ruwa da tsaki na Yammacin Nasarawa sun bayyana kudurinsu yayin da suka kai ziyarar hadin gwiwa ga Sule a gidan Gwamnati.
Sanata Adamu ya ce yankin ya gamsu da shugabancin Sule ta fuskar yada ribar dimokiradiyya a fadin jihar.
Adamu ya ce sun je gidan gwamnatin ne musamman don yaba wa Gwamnan saboda kyakkyawan jagoranci da ya nuna tare da sake nuna biyayyarsu ga gwamnatinsa.
“Mun zo nan ne domin mu gaya wa duniya cewa ba mu da wani daga yankinmu da zai fafata da kai, kai ne dan takararmu a 2023,” in ji shi.
Ya gabatar da kudirin nuna goyon baya ga kudurin ne bayan da mambobin majalisar daga shiyyar suka mara wa Sule baya a matsayin dan takarar yankin suka a 2023.
Gwamnan ya nuna godiyarsa ga nuna kauna da shiyyar ta Nasarawa ta Yamma, ya jaddada babban burinsa shi ne tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jihar.
Gwamnan ya ce zai ci gaba da nuna godiya ga magabacinsa Sanata Umaru Tanko Al-Makura, wanda ya ba shi goyon baya a duk tafiyar da ya yi zuwa gidan Gwamnati.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *