fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Gwamna Tambuwal ya amince da ware N4bn domin yin wasu ayyuka a bangaren lafiya da Ilimi a Jihar Sakkwato

Gwamnatin jihar Sakkwato yayin taron majalisar zartarwar ta jihar, a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Tambuwal a ranar Laraba, ta amince da kashe Naira biliyan 4 don inganta ayyukan kiwon lafiya biyu da kuma na ilimi guda daya a jihar.

Majalisar ta kuma soke wasu kwangiloli guda biyar da aka yi watsi da su wadanda suka hada da gina karin bangarori biyu na unguwanni, gyaran, gina gidajen ma’aikata 47 da kuma kammala aiki na musamman, wanda ya hada da gidan wasan kwaikwayo, dakin ajiye gawarwaki da sauransu a asibitin Murtala Muhammad da ke Sakkwato.

Hakanan an soke kwangilar gina Babban Asibiti a garin Wamakko wanda aka bayar tun shekarar 2013.

Sabbin ayyukan da aka shirya aiwatarwa sune: gina asibitin Premier ta Binji da gina dakin kwanan dalibai mai daukar gadaje 608 a Sultan Abdur-Rahman School of Health Technology, Gwadabawa da kuma gina katafaren dakin kwanan dalibai mai bene a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari (SSCOE).

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Ali Inname da na Ilimi mai zurfi, Farfesa Bashir Garba, sun ce an amince da kashe sama da Naira biliyan 2 da miliyan 700 don gina Babban Asibitin a karamar hukumar Binji, an shirya kammala shi cikin watanni 17.

Kwangilar Kwalejin Shehu Shagari (SSCOE) za ta lakume sama da Naira miliyan 524 yayin da ta Sultan Abdul Rahman School of Health Technology, Gwadabawa za ta cinye sama da Naira miliyan 523, ana sa ran za a kammala su a cikin watanni tara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *