Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kanone yayi zarra a fannonin habaka harkar Ilimi da kuma harkar kiwon lafiya a tsakanin gwamnonin Najeriya, kafar watsa labarai ta New telegraph ce ta karramashi da wannan kyauta ta musamman.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Gwamnan ya bayyana jin dadinshi da kuma murna a kan wannan karramawa da akamishi. A daren jiyane dai akayi wannan taron na karrama fitattun mutane da New Telegraph ta shirya a birnin Legasa.
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal shima ya samu kyautar karramawa ta gwamnan gwamnoni na shekara.
Muna tayasu murna.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});