fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamna Wike na jihar Rivers ya kori babban sakatare saboda karya dokar Coronavirus/COVID-19

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya kori wani babban sakataren gwamnatinsa saboda karya dokar Coronavirus/COVID-19.

 

Sanarwar korar ta bayyana cewa babban Sakataren, Sunny Okere ya halarci wata jana’iza ce da mutane sama da 50 suka halarta wanda ya sabawa dokar gwamnati.

Sannan kuma ma’aikatan dake kula da tabbatar da dokar gwamnatin sun je su hana taron amma babban sakataren ya koresu.

 

Dan hakane gwamna Wike yace ya koreshi daga aiki nan take kuma yana fatan sauran mutane zasu dauki darasi akan hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.