Gwamnatin jihar Rivers ta dauki matakin hana gidajen rawa na dare sannan kuma ta hana karuwanci.
Gwamnan jihar, Nyesome Wike ne ya bayyana haka a sakon sabuwar shekara da ya saki.
Gwamnan yace matakin zai dakile koyawa matasa abubuwan bata tarbiyya wanda basu dace ba.