fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana dalilin da yasa Fani-Kayode bai koma APC ba

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana dalilin da yasa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode bai koma jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ba.

Bello ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin mai suna “Siyasar Mu A Yau.”

Idan zaku tuna an ruwaito cewa Yahaya Bello, a cikin bidiyo na mintina biyu, yayi ikirarin cewa tsohon ministan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Amma, Fani-Kayode ya karyata rahotannin da ke cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, ya ce ganawar da gwamnonin biyu ba ta da alaka da sauya sheka.

Karanta wannan  APC ta shigar da karan Tinubu a kotu cewa ta hana shi tsayawa takarar shugaban kasa

Bello ya ce, ni da Cif Fani-Kayode‘ yan uwan ​​juna ne kuma muna hada gwiwa wajen tabbatar da an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar.

Ya kara da cewa shigarsa APC ko rashin shigarsa, wannan ra’ayinsa ne, rarrabuwar kawunan jam’iyyun siyasa ba shi da wata alaka da su biyun da ke aiki don hadin kai, zaman lafiya da ci gaban kasar nan, wannan shi ne kadai abin da ya sani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.