Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jinjinawa Sojojin Najeriya bisa dakile harin da Boko Haram suka yi yunkurin kai musu a Marte.
Sojojin Najeriya sun sanar da dakile harin na ranar Asabar inda suka kashe Boko Haram din da dama.
Gwamna Zulum ya bayyana jinjinar ne ta bakin mataimakinsa, Umar Kadafur a yayin ziyarar da ya kai Marte dan jajantawa mutanen yankin kan harin. Yace Gwazon sojojin abin a yaba ne.
Ya kuma bukaci mutanen garin da su dauki lamarin a matsayin kaddara daga Allah.