fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Gwamna Zulum Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Samu Tikitin Kai Tsaye A Jam’iyyar APC

Daga Abubakar A Adam Babankyauta

Jam’iyar APC ta rufe siyar da fom din tsayawa neman takarar kowace kujera na zaben 2023.

Kawo yau da aka rufe sayar da Fam, Zulum da gwamnoni biyu ba su da abokan hamayya a cikin jam’iyar ta APC.

Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa jam’iyar APC ta rufe sayar da fom din takara ga masu neman kujerar mulki karkashin inuwar ta a zaben kasa da za a yi a 2023.

Idan kun tuna jam’iyyar ta APC ta fara sayar da fom din ne a ranar 26 ga watan Afrilu, 2022 inda ta rufe siyar da fom din a yau Talata 10 ga watan Mayun.

Jam’iyar ta APC ta siyar da fom din takarar kujerar shugaban kasa akan kudi har Naira Miliyan 100 na gwamna Naira Miliyan 50 yayinda masu neman kujerar Sanata Naira Miliyan 20 na yan Majalisar wakilai Naira Miliyan 10 sannan yan Majalisun jihohi kuma Naira Miliyan 2

Karanta wannan  Hotunan yanda gwamna Ganduje ya rabawa wanda bam din Sabon gari ya tashi da danginsu diyyar Miliyan 1 kowane

Kawo yau da jam’iyar ke rufe siyar da fom din akwai gwamnoni uku da basu da abokan hamayya a cikin jihohin su a karkashin jam’iyar ta APC.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum na daya daga cikin gwamnonin da basu da abokan hamayya a cikin jam’iyar ta APC sai kuma; Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahaman Abdulrazak

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.