A yau ranar lahadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.
Kuma an samu labari daga najiya mai karfi cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ne ya cewa Tinubu ya zabi uban gidan nasa a madadinsa.
Rahotanni da dama sun bayyana a kwanakin baya cewa Zulum da Shettima ne mutane biyu da Tinubu ke son dauka a matsayin abokin takararsa.
Kuma a yau ya gana da shugaba Buhari a Daura ya bayyana masa cewa ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takarar nasa.